Ina aka kwana wajen kare hakkokinmu da kuma kyautata rayuwarmu a Najeriya? – NNDF

0 112

Yayin da Najeriya ke murnar cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, masu bukata ta musamman a kasar sun yi waiwaye kan inda aka kwana wajen kare hakkoki da kuma kyautata rayuwarsu a kasar.

Masu lalurar nakasa ko bukata ta musamman sun yi waiwayen ne a yayin wani taro da suka gudanar a birnin Kano karkashin inuwar kungiyar Northern Nigeria Disability Forum (NNDF).

A yayin taron, sun yi duba game da abubuwa da dama ciki har da batun ilimi da lafiya da rabon tattalin arzikin kasa dama harkar zaman takewa.

Cikin abubuwan da suka gano shi ne har yanzu masu bukata ta musamman na fuskantar matsaloli wajen harkar zaman takewa kamar yadda Yarima Sulaiman Ibrahim, shugaban kungiyar ya shaida wa BBC.

Yarima Suleiman Ibrahim, ya ce kundin tsarin mulkin kasa ya bayar da damar samun ‘yanci, amma a bangaren wannan ‘yancin ba a la’akari da masu bukata ta musamman.

Shugaban kungiyar, ya ce “Ko shakka babu an samar da hukumar da ke kula da masu bukata ta musamman, to amma har yanzu bata yin abin da ya kamata ace ta yi saboda har yanzu mutanensu na bara a kan titi, to da ace hukumar na aikin da ya dace to ba za a ga masu bukata ta musamman na bara a kan titi ba.

Shugaban kungiyar (NNDF), ya ce yanzu za su yi fito na fito da matsalolin da ke damunsu don su tunkaresu da gaske.

Leave a Reply

%d bloggers like this: