Hukumar WHO ta bayyana damuwarta cewa kashi 36 cikin 100 na dukkan mace-macen cutar tarin fuka na faruwa a nahiyar Afirka

0 168

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana damuwarta cewa kashi 36 cikin 100 na dukkan mace-macen cutar tarin fuka na faruwa a nahiyar Afirka kuma rashin samar da kudaden yaki da cutar zai yi matukar tasiri ga kasashen Afirka.

Hukumar ta ce karuwar saka kudade zai iya canja halin da ake ciki ta hanyar rage wahalhalun da ake sha tare da mutuwar miliyoyin mutane.

Daraktar hukumar ta WHO a Afirka, Matshidiso Moeti ce ya bayyana hakan a cikin wani sako da ta fitar domin tunawa da ranar tarin fuka ta duniya da ake gudanarwa a ranar 24 ga Maris na kowace shekara.

Matshidiso Moeti ta ce an ware ranar ne domin wayar da kan jama’a da fahimtar juna game da daya daga cikin cututtukan da suka fi kashe mutane a duniya.

Ta ce shugabannin manyan kasashen duniya na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da tara dala biliyan 13 a duk shekara domin bayar da tallafin rigakafin cutar tarin fuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: