Hukumar NDLEA Ta Kama Dan Kasar Suriname Da Laifin Safarar Hodar Ibilis A Nigeria
Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wani mutum ɗan ƙasar Suriname da ke yankin kudancin Amurka, bisa laifin safarar hodar ibilis a Najeriya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama Dadda Lorenzo Harvey Albert da hodar ibilis ɗin da nauyinta ya kai kilogiram 9.9, wadda ya ƙunshe a cikin kwaroron-rabo tare da saka ta cikin ƙwalaben turare.
Hukumar ta ce ta kama mutumin mai shekarar 34 a filin jirgin saman birnin Fatakwal, a lokacin da ya shigo da ƙulli 117 na hodar ibilis.
Hakan na zuwa a daidai lokacin da hukumar ta ce ta ƙwace kilogiram 1,559.3 na tabar wiwi a faɗin jihohin biyar, tare da ƙwace ƙwayar tramadol kimakin 648,050 a jihohin legas da imo da kuma taraba.