Hukumar NDLEA sun yi nasarar kame kilogiram 991 na miyagun kwayoyi a jihar Jigawa

0 338

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a jihar Jigawa ta jaddada kudirin ta na dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a cikin al’umma duk da irin harin da ake kaiwa jami’anta a lokacin gudanar da ayyukan su.

Kwamandan Hukumar na jihar Jigawa, Alhaji Mu’azu Aliyu Dan-Musa ya bada wannan tabbaci a lokacin taron bikin zagayowar ranar hana ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Duniya ta bana da aka gudanar a ofishinsa

Ya yi bayanin cewa sun yi nasarar kame kilogiram 991 na miyagun kwayoyi, tare da kama mutane 422 da ake zargi a wannan shekarar da suka kunshi Maza 109 da kuma Mata 13, yayinda aka zartar da hukuncin dauri akan guda arba’in da hudu.

Alhaji Mu’azu Dan-Musa ya ce a kokarinsu na ceto rayuwar Matasa da kuma jihar jigawa daga ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Hukumar ta dukufa wajen gudanar da sintiri akai-akai tun daga watan Yuni na shekarar bara zuwa yanzu, inda ta samu nasarar kamawa da kuma kwace kayayyakin maye masu yawa.

Haka kuma, sun dukufa wajen shelar wayar da kan mutane a tashoshin mota da makarantun sikandire da kuma na gaba da sikandire illolin ta’ammali da miyagun kawayoyi.

Leave a Reply