Hukumar NDLEA na neman wata sarauniyar kyau ta shekarar 2015 ruwa a jallo

0 172

Hukumar yaki da sha da fataucxin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana wata sarauniyar kyau a shekarar 2015 a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo saboda zarginta da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Bayanai na cewa Aderinoye Queen Christmas da aka fi sani da Sarauniya Oluwadamilola Aderinoye ta tsere wa jami’ai daga hukumar yaƙi da sha da fataucin haramtattun ƙwayoyi, NDLEA a lokacin da suka kai samame gidanta da ke Legas a makon da ya gabata.

Cikin wata sanarwa, hukumar ta ce an kai samamen ne bayan wasu sahihan bayanai da suka nuna cewa tsohuwar sarauniyar kyan tana da hannu a ta’amali da haramtattun kwayoyi. Wadda ake zargin ta taba lashe gasar kyau ta Miss Commonwealth Nigeria Culture a shekarar 2015/2016 kuma ita ce ta kafa gidauniyar Queen Christmas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: