Hukumar NCDC tace ƙarin mutum 418 suka kamu da cutar korona a Najeriya

0 307

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta NCDC ta tabbatar samun ƙarin mutum 418 da suka kamu da korona ranar Lahadi a ƙasar.

Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce mutanen sun fito ne daga jiha 12. Jihohin su ne:

  • Lagos-314
  • Ogun-27
  • Plateau-18
  • Edo-17
  • Enugu-11
  • Abia-8
  • Delta-7
  • Bayelsa-5
  • Kano-4
  • Rivers-4
  • Osun-2
  • Oyo-1

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 217,481 ne suka harbu da cutar tun bayan ɓullarta. Haka nan ta kashe 2,981, sai kuma mutum 207,746 da aka sallama bayan sun warke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: