Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana damuwa kan yawan mata masu dauke da juna biyu da suka samu zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.
Shugaban tawagar likitocin Najeriya Dr Usman Galadima ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Usman Galadima ya ce sai da aka taimaka aka kwantar da daya daga cikin matan masu juna biyu, yayin da wasu kuma sai da aka kai su asibitin mata domin samun kulawar da ta dace.
Ya nanata cewa bai dace a dabi’ance ba a bar mata masu juna biyu su tafi aikin hajji saboda wahalhalu, da hadari da barazanar lafiyar da za su iya fuskanta, ko kuma su gamu da matsaloli a lokacin aikin.
Shugaban tawagar likitocin ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu alhazai da ke fama da rashin lafiya suka zo kasa mai tsarki ba tare da sahihan magungunansu da aka amince da su ba.