Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce hukumar tana ƙoƙari domin tabbatar da kuɗin Hajjin bana bai kai yadda ake hasashe ba, inda ya ce abin da yake fata shi ne ragowa.
Hukumar ce ta sanar da cire tallafin da take bayarwa a kan kuɗin Hajjin duk shekara, wanda a sanadiyyar hakan masana suka ce kuɗin kujerar Hajjin zai iya haura naira miliyan 10.
A zantawarsa da BBC, sabon shugaban hukumar, Saleh Usman, wanda aka fi sani da Saleh Pakistan ya ce, “ba sa fatan a samu ƙarin kuɗin kujerar Hajji kamar yadda ake hasashe, za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin hakan bai faru ba, kuma suna fata in sha Allah ba zai kai haka ba.
Ya kara da cewa abin da suke fata shi ne a samu ragowa daga farashin kuɗin kujerar da aka biya a bara, kuma suna fata da yardar Allah za’a samu nasara.”