Hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa ta karbi ₦7.7Bn na tallafin annobar korona

0 142

Shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa ta Olubunmi Kuku yace hukumar ta karbi Naira Bilyan 7.7 a matsayin kudin tallafin annobar korona.

Shugabar hukumar ta bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a da kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar ya shirya.

Ta kara da cewa shekarar 2020 ta zo da manyan kalubalai lamarin da ya shafi ayyukan hukumar.

Tae idan za’a iya tunawa a watan Maris din shekarar 2020,hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar Korona a matsayin annobar duniya. Olubunmi Kuku tace ayyana cutar a matsayin annobar ya shafi ayyukan hukumar sosai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: