An kashe N200Bn domin shirye-shiryen kidayar jama’a cikin shekaru 8

0 407

Hukumar kidaya ta kasa a jiya ta ce an kashe naira biliyan 200 domin shirye-shiryen kidayar jama’a cikin shekaru takwas.

Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Isiaka Yahaya, ya ce maganar da aka yi na cewa an kashe kudaden ne a ‘yan shekarun da suka gabata kuskure ne ganin yadda hukumar ke shirin kidayar jama’a tun shekarar 2014.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja.

Isiaka Yahaya ya ce an kashe makudan kudaden ne wajen shirye-shirye daban-daban domin tabbatar da cewa aikin kidayar ya samar da sahihin bayanai masu inganci.

Ya bayyana cewa babban aikin da aka kashewa kudi shi ne kayyade wuraren kidayar jama’a domin a samu saukin aikin wanda hakan ya baiwa kasar bayanan adadin gidajen da ke kasar nan.

Aikin kidayar Najeriya da yakamata a gudanar da ita tun shekarar 2016 bisa ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya an sha dagata saboda wasu dalilai tun bayan gudanar da ita a shekarar 2006.

Leave a Reply

%d bloggers like this: