Hukumar Kare Haƙƙin dan adam ta Najeriya ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 106,604 a watan Yunin 2024

0 112

Hukumar Kare Haƙƙin dan adam ta Ƙasa a Najeriya ta ce ta karɓi jimillar ƙorafi 106,604 da suka danganci take haƙƙi a watan Yunin 2024 kaɗai.

Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin “abin damuwa kuma wanda ba ta taɓa gani ba”, tana mai cewa yankin arewa ta tsakiyar Najeriya ce kan gaba da da lamurra 29,462.

Da yake gabatar da rahoton wata-wata a karo na shida ga manema labarai ranar Litinin, Babban Sakatare a hukumar Anthony Ojukwu ya ce sun samu rahotonnin kisan kare dangi, da satar mutane, da ayyukan ƙungiyar asiri a jahohin Bauchi, da Katsina, da Neja,Kaduna, Filato,  Borno, Binuwai, da kuma Edo.

Haka nan a cewarsa, an samu tauye haƙƙin ɗan’adam sau 18,458 a yankin kudu maso yamma, da kuma 15,101 a arewa maso yamma, sai 12,907 a arewa maso gabas, yayin da aka samu mafi ƙaranci a kudu maso gabas da 9,164. Mista Ogbonna ya ƙara da cewa sun samu badaƙalar jefar da yara 1,667, sannan sun samu ƙoranfin fyaɗe 58, da kuma cin zarafi ta hanyar lalata a gida da waje sau 600 cikin watan na Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: