Hukumar JAMB ta kara kudin rijistar jarrabawar UTME na shekarar 2024

0 352

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta kara kudin rijistar jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) na shekarar 2024.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta JAMB ta fitar, ta bayyana sabon kudin rajistar jarabawar ta UTME tare da jarabawar Mock da ya kai naira dubu bakwai da dari Bakwai Kacal.

Yayin da sabon kudin jarabawar UTME ba tare da jarabawar Mock ba, ya kasance Naira dubu shida dari biyu Kacal . Ana sa ran hukumar ta JAMB za ta yi cikakken bayani kan wadannan kudade  ranar 15 ga Janairu, 2024 ko kuma kafin wannan rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: