Hukumar INEC ta biya diyya ga wani jami’inta da ya ji rauni a lokacin zaben 2023

0 32

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta mika tallafin diyya ga wani jami’inta da ya ji rauni a hatsarin da ya faru a lokacin zaben 2023 a Jihar Bauchi. 

A cikin wata sanarwa da INEC reshen jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook a jiya Alhamis, an bayyana cewa shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya gabatar da kudin diyya yayin taron mako-mako na shugabannin hukumar. 

Wakilinsa, Kwamishinan Zabe na Jihar Bauchi, Muhammad Nura, ya mika takardar cakin kudin na naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da hamsin (₦1,250,000) ga Adamu Yusuf, jami’in tattara sakamakon zabe daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, wanda ya ji rauni a kafarsa sakamakon hatsarin mota da ya afka masa a lokacin zaben. 

Adamu Yusuf ya nuna matuƙar farin ciki da godiya ga INEC bisa wannan tallafi, yana mai cewa hakan na nuna kulawar hukumar kan walwalar ma’aikatanta yayin gudanar da zabuka.

Leave a Reply