Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta hada hannu da masu amfani da shafukan TikTok

0 265

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada hannu da masu amfani da shafukan TikTok domin tsaftace harkokinsu na sada zumunta a kokarinta na dakile yawaitar munanan dabi’u a tsakanin jama’a da ke amfani da kafafen sadarwa na zamani.

Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine ya bayyana hakan a lokacin wani taro da hukumar ta yi da TikTokers a jihar.

Yayin da ya ke bayyana cewa taron na da nufin sauya tunanin TikTokers wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani daga mara kyau zuwa mai kyau.

Ya ce gwamnatin jihar Kano na shirin baiwa masu amfani da shafin TikTok karfin gwiwa wajen gyara tsarin da kuma mayar da shi hanyar samun kudi.

Yawancin masu amfani da shafin na TikTok waɗanda suka yi jawabi lokacin taro da City & Crime waɗanda suka lura cewa sun gamsu da taron, sun yi alkawarin canza halayensu. Daga nan ne hukumar Hisbah ta baiwa kowane daya daga cikin mahalarta taron sama da dari biyu kudin mota Naira dubu 2,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: