Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata sama da kwalaben barasa miliyan 3 da dubu 800 da ta kwace a watannin baya.
Babban kwamandan hukumar Dr Harun Ibn-Sina ne ya bayyana haka a jiya a yayin lalata giyar da aka kama a Tudun Kalebawa a karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar.
Haruna Ibn-Sina ya bayyana cewa hukumar na samun nasara a yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da abubuwan sa maye da duk wasu munanan dabi’u na al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar ta amince da lalata kayan maye, don haka aka gudanar da aikin lalata su.
Ya yabawa gwamnatin jiha bisa jajircewarta wajen ganin an magance matsalolin al’umma.
Hakazalika, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya nanata kudirin gwamnatin jihar na kyautata jin dadin ma’aikatan hukumar.
Ganduje ya samu wakilcin dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Albasu a majalisar dokokin jihar kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin addini Sunusi Usman-Batayya.