Hukumar Hisbah ta damke wasu mutane biyar ‘yan luwadi a Kano

0 339

Hukumar ta Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da luwaɗi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso ta cikin gari.

Kamar yadda majiyar mu ta ruwaito, shugaban hukumar Malam Haruna ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 12 ga Yulin wannan ashekarar ta 2021.

A cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

“Duka wadanda ake zargin sun haura shekara 20, mun kuma kama su ne a ranar 11 ga watan Yuli a wani samame na musamman,” in ji shi.

A karshe ya karkare da cewa za a mika wadannan mutane da aka kama zuwa kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: