Kwamatin sake fasalin ayyukan hakumar Hisbah ya bukaci hadin kai da goyon bayan hakumar yansanda da hakumar tsaron farin kaya ta DSS domin bunkasa ayyukan su a fadin jihar jigawa.
Shugaban kwamain kuma sakatyaren gwamnatin jihar jihar Jigawa, Mallam Bala Ibrahim ya yayi wannan rook lokacin da ya jagoranci mambobin kwamatin zuwa wata ziyarar aiki ga kwamashinan yan sanda da daraktan hakumar tsaron farin kaya ta DSS.
Yace wasu daga cikin ayyukan hakumar Hisban sun hada yaki da munanan dabi’u da sasanton ma’aurata da kuma bayar da agajin gaggawa da kuma kawar da ayyan masha’a da sauransu.
Mallam Bala ya bayar da tabbatacin cewa hakumar sa zata karfafa alaka mai karfi tare da aiki kafada-da-kafada da hakumomin tsaro a dukkan fadin jiha.
Da yake mayar da jawabi kwamashinan yan sadan AT. Abdullahi ya tabbatar da shirinhakumar yansandan jihar Jigawa na yin hadin guiwa da Hisba domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a. Kwamatin ya kuma kai makamanciyar ziyarar ga ofishin babban Alkalin Jiha mai sharia Umar Maigari Sadik, da babban alkalin alkalan jiha Muhammad Sani Salihu.