Hukumar EFCC ta sake bankaɗo wani sabon asusun Diezani dauke da fiye da Dala miliyan 72
Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC tace ta bankado wani sabon asusun ajiyar tsohuwar ministar man fetur din kasar Diezani Allison Madueke dake dauke sama da Dala miliyan 72 a Bankin Fidelity.
Hukumar EFCC ta bayyana haka ne bayan ta damke tsohon shugaban bankin Nnamdi Okonkwo wanda ya jagoranci shi lokacin da Madueke ke rike da mukamin minista a cikin kasar.
Tsohuwar ministar wadda ke cikin na sahun gaba gaba a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da ta shude ta gudu daga Najeriya domin kaucewa tuhume tuhume da dama da ake mata akan zargin cin hanci da rashawa, yayin da Hukumar EFCC ta kwace wasu daga cikin kadarorin da ta mallaka.
Mai magana da yawun Hukumar Wilson Uwujaren ya sanar da gano kudaden a asusun ajiyar Diezani da kuma kama kama tsohon manajan bankin.
Uwujaren yace an kuma yiwa Okonkwo wanda yanzu ke jagorancin Bankin First Holding tambayoyi dangane da wasu kudaden da suka kai Dala miliyan 153 da wasu Dala miliyan 115 na daban.
Kakakin hukumar yace tuni suka kwato Dala miliyan 153 daga ajiyar ta, yayin da ake ci gaba da tafka shari’a akan Dala miliyan 115 wanda ake zargin an ware su ne domin baiwa jami’an Hukumar zabe cin hanci.
Uwujaren yace yanzu haka Okonkwo tare da wani Charles Onyedibe na komar EFCC saboda sabon asusun ajiyar dake kunshe da sama Dala miliyan 72 da aka gano.
Asalin Rahoton:
https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20211216-efcc-ta-gano-wani-sabon-asusun-diezani-dauke-da-dala-miliyan-72