Hukumar EFCC ta kama wani a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da katunan ATM guda 576

0 208

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta kama wani da ake zargi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da katunan ATM guda 576.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau ta hannun mai magana da yawun ta, Wilson Uwujaren, ta ce sabon kamen ya zo ne sa’o’i biyu kacal bayan ta cafke wasu mutane uku da aka kama da katunan ATM guda dubu 1 da 144 a filin jirgin saman.

Uwujaren ya ce jami’an hukumar tare da hadin gwiwar jami’an tsaron hukumar jiragen sama da na hukumar kwastam a karkashin rundunar ta musamman dake yaki da safarar kudade ne suka kama wanda ake zargin mai suna Khalil Bashir Lawal a jiya.

Da aka kama shi, an gano cewa Khalil Lawal wanda ya je kasar Uganda ta kamfanin jiragen saman kasar Habasha, ya boye katunan ATM guda 576 masu dauke da sunaye daban-daban na bankuna daban-daban a cikin kayansa.

Sanarwar ta EFCC ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: