Hukumar dake kula da aikin shari’ah ta yaye lauyoyi 884 domin aikin lauya a Najeriya

0 210

Hukumar dake kula da aikin shari’ah a kasarnan ta yaye lauyoyi 884 domin aikin lauya a Najeriya inda ta gargade su da su kiyaye wajen bin dokoki da ka’idojin aikin lauya.

A jiya aka fara bikin kwanaki uku na yaye lauyoyin rukunin watan Yuli, inda lauyoyi 880 suka sha rantsuwa a Abuja.

Sabbin lauyoyin sun samu nasara a jarabawar karshe ta watan Disambar 2020, wacce suka rubuta a makarantar aikin lauya ta kasa, a karkashin kulawar hukumar dake kula da aikin shari’ah.

Shugaban hukumar lauyoyi ta kasa, Bode Rhodes-Vivour, ya shawarci sabbin lauyoyin da su zamo dattawa kuma su kauracewa dukkan abinda zai bata sunan aikinsu.

A wani labarin kuma, kwamitin hukunta masu aikin shari’ah ya hukunta lauyoyi 11 a kasarnan bisa take dokokin aikinsu a bana.

Shugaban hukumar lauyoyi ta kasa, Bode Rhodes-Vivour, ya sanar da adadin lauyoyin da aka hukunta bisa take dokoki a bikin yaye sabbin lauyoyi da aka gudanar a dandalin Eagle Square dake Abuja a jiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: