Hukumar Civil Defence ta shawarci Al’umma su kasance masu lura da tsaro a lokacin bikin Sallah a Jigawa
Hukumar tsaron farin kaya ta kasa Civil Defence reshen jihar Jigawa, ta gargadi al’ummar jihar da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.
Kwamandan jihar Musa Alhaji Malah ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar CSC Adamu Shehu.
Ya ce rundunar ta tura jami’ai 1,125 domin samar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a kafin bikin Sallah da kuma bayan Salah.
Kwamandan ya ce hakan ya yi daidai da umarnin kwamandan rundunar na kasa wajen sanya ido na tsawon sa’o’i 24 domin kare rayukan fararen hula a fadin kasar nan.
Ya kuma umarci kwamandojin yankin, jami’an runduna, da kwamandojin sassa daban daban da su tabbatar da bin ka’idojin aiki. Kwamandan, ya shawarci mazauna jihar Jigawa akan su kasance masu bin doka da oda tare da bawa jami’an tsaro hadin kai don yin bikin ba tare da wata matsala ba.