Hukumar asusun adashen gata na ƴan fanshon jihar Jigawa ya ƙaddamar da biyan haƙƙokin ma’aikata kuɗinsu da ya haura Naira miliyan 219

0 286

Hukumar asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan Hukumomin jihar Jigawa ya kaddamar da biyan hakkokin maaikata na jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen ilmi da kudinsu ya haura naira Miliyan 219.


Hakkokin maaikatan da za a biya sune na wadanda suka yi ritaya daga aiki dana magada da cikon kudaden fansho ga yan fanshon da suka rasu basu cika shekaru biyar suna karbar fansho ba da kuma mayarwa da maaikata kudadensu na adashen gata da suka tara.


Sakataren zartarwa na asusun Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da biyan hakkokin maaikatan a harabar asusun dake pension house.


Yace za a biya giratuti ga maaikatan jiha da kananan hukumomi dana sashen ilmi163 da suka yi ritaya daga aiki a watan jiya tsabar kudi naira miliyan dari hudu da ashirin da biyu da dubu dari uku da goma sha uku.


Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya kara da cewar za a biya magadan maaikatan jiha dana kananan hukumomi da kuma na sashen ilmi 33 da suka rasu, hakkokinsu da ya tasamma naira miliyan hamsin da bakwai da dubu dari da casein da shida.


Yayinda za a biya naira miliyan 18 ga iyalan yan fansho da suka rasu basu cika shekaru biyar suna karbar fansho ba
Inda kuma ya yabawa gwamna Badaru Abubakar bisa kulawar da yake yiwa asusun a kowane lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: