Hukumar agajin gaggawa ta jihar Katsina tace sama da gidaje dubu 1500 ne mamakon ruwan sama ya shafa

0 208

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Katsina tace sama da gidaje dubu 1 da 500 ne mamakon ruwan sama ya shafa a kananan hukumomi 3 na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Mohammed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Katsina cewa daga cikin adadin, akwai sama da gidaje 800 a Faskari da 400 a Bindawa da kuma 300 a karamar hukumar Sabuwa.

Yayi bayanin cewa a karamar hukumar Bindawa, mamakon ruwan saman kamar da bakin kwarya, wanda aka shafe sama da awanni 5, ya jawo mutuwar mutane 2, inda yace hukumar na duba hanyoyin tallafawa wadanda lamarin ya shafa.

Kamfanin dillancin labaran ya tunatar da cewa mamakon ruwan saman da aka fara da misalin karfe 10 na safiyar ranar Litinin, ya kai har wajen karfe 4 na yammacin ranar, ya tursasawa masu ababen hawa kauracewa abin hawarsu.

Wasu daga cikin mazauna birnin Katsina, da suka zanta da manema labarai sun bayyana damuwa bisa ambaliyar ruwa a wasu titunan birnin saboda mamakon ruwan sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: