Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Ali Pate, ya ce sauran kasashe na daukar ma’aikatan lafiya da suka bar Najeriya zuwa kasashen ketare ne saboda irin horon da ma’aikatan kiwon lafiyar suka samu a Najeriya.
Pate ya bayyana haka ne yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa ta shirya a Abuja.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su karfafa ‘ya’yansu su karanci kwasa-kwasan likitanci sannan ya bukaci jihohi su samar da cibiyoyin horar da likitoci da ma’aikatan jinya domin cike gibin da wadanda suka bar kasar nan.
Ministan lafiyan ya kuma yaba wa wadanda suka yanke shawarar dawowa gida najeriya domin yi wa kasa hidima.
Ya ce akwai ma’aikatan lafiya da dama da za su iya barin kasar nan amma sun tsaya domin suna son su ba da gudummawa a Najeriya.
- Comments
- Facebook Comments