Harkokin koyo da koyarwa sun durkushe a ABU Zariya sakamakon matsalar wutar lantarki

0 226

Harkokin koyo da koyarwa sun durkushe a jami’ar Ahmadu Bello Zariya inda dalibai suka zauna a gida kusan wata guda sakamakon matsalar wutar lantarki da ta addabi jami’ar.

Bincike ya nuna cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric na bin jami’ar bashin makudan kudade, wanda hakan ya sa kamfanin ya yanke wutar lantarki a jami’ar a ranar 15 ga watan Mayun 2023.

Har ila yau jami’ar na kokarin biyan kudaden alawus-alawus na ‘yan fansho sama da dari da suka yi nasara a kan jami’ar a wata shari’ar da aka yi kwanan nan.

An gano cewa hukumar makarantar ta biya naira miliyan 40 daga cikin bashin kudin wutar lantarkin.

Sai dai har yanzu kamfanin na Kaduna Electric bai mayar da wutar ba, duk da kudin da aka biya, wanda hakan ya tilastawa mahukuntan jami’ar dakatar da duk wasu harkokin karatu.

A wata sanarwa da aka buga a ranar 15 ga watan Mayu, hukumar jami’ar ta ce an dakatar da karatun dalibai na zangon karatu na biyu da aka tsara komawa a ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: