Harin kwanton bauna yayi sandiyyar mutuwar wani dan sanda a jihar Yobe

0 298

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi wa tawagar jami’an tsaron jihar Yobe kwanton bauna a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe dan sanda daya tare da jikkata wasu shida.

An kai harin ne a hanyar Jakana zuwa Mainok a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar jami’an tsaron sun raka gwamnan zuwa Maiduguri domin halartar  taro karo na 24 na jami’ar Maiduguri, inda aka baiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima digirin girmamawa. Yayin da tawagar ta koma Yobe, an ce Gwamna Mai mala Buni ya tsaya a Maiduguri kafin tafiya Abuja don wata ganawa a hukumance.

Leave a Reply

%d bloggers like this: