Harin da Iran ta kai wa Isra’ila ‘ɗan ƙaramin hukunci ne’ – Khamenei

0 176

Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yaba da hare-haren da Iran ta ƙaddamar kan Isra’ila ranar Talata, inda ya kira su da cewa hare-hare da ke kan ‘ƙa’ida”.

Yayin da yake gabatar da huɗumar Juma’a a birnin Tehran, Mista Khamenei ya ce abin da suka yi ”ɗan ƙaramin hukunci” ne kan Isra’ila saboda ”laifukan ban mamaki da take aikatawa”

Ya kira Isra’ila da mulkin “masu shan jini” da Amurka a matsayin “mahaukacin kare” a yankin.

Mista Khamenei – wanda ke gabatar da huɗubar Juma’arsa ta farko cikin kusan shekara biyar – ya ce Jamhuriyar Musulunci za ta ɗauki ”matakin da ya dace” kan Isra’ila da ”ƙarfin tuwo”.

Ya jaddada cewa Iran ba za ta lamunci ”sassauci” ko ”ɗaga ƙafa” kan Isra’ila ba.

Ayatollah Khamenei wanda ya yi jawabin nasa a harshen Farsi ya jaddada cewa “haɗin kan” Musulmin duniya bisa tafarkin Alƙur’ani shi ne abin da ya zamanto wajibi a tsakanin Musulmi.

“Maƙiyan Iran su ne dai maƙiyan Falasɗinawa da Lebanon da sauran ƙasashen Musulmin duniya.” In ji Khamenei.

Kafafen watsa labaran ƙasar ta Iran sun rawaito cewa Ayatollahi Khamenei zai yi wani jawabi da harshen Larabci domin al’ummar Lebanon da Falasɗinu.

Jawabin shugaban addinin na ƙasar Iran dai na zuwa ne kwana uku kafin cikar hare-haren da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, sannan kuma kwanaki uku bayan harin makamai masu linzami da Iran ɗin ta kai Isra’ila.

Wannan dai ita ce huɗuba da Khamenei ya yi karo na biyu tun bayan wadda ya yi lokacin da aka kashe Janar Qasem Soleimani a 2020.

  • BBC Hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: