Hare-haren ‘yan bindiga a jihar Filato ya sa daruruwan mutane sun rasa matsugunansu

0 334

Akalla kauyuka 17 ne a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato da suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren baya-bayan nan da aka sake tsugunar da su domin mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa gidajen kakanninsu.

Babban kwamandan runduna uku na rundunar sojojin Najeriya kuma kwamandan Operation Safe Haven a Mangu, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana hakan a lokacin rabon kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar da har yanzu ba su koma garuruwansu ba.

Hare-hare na baya bayan nan da ‘yan bindiga suka kai kauyukan, ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da kuma daruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu tun na iyaye da kakanni. ‘Yan gudun hijirar da suka warwatsu sassa daban-daban na karamar hakumar ta Mangu na cikin matsanancin yanayi inda gwamnatin jihar da jama’a da kungiyoyin da suka damu suka ba da agaji domin rage radadin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: