Har yanzu bani da yarjejeniya da wani dan takara a zaben 2023 – Wike

0 224

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce shi da abokansa da aka fi sani da G-5 ba su kulla yarjejeniya da wani dan takarar shugaban kasa ba gabanin zaben 2023 ba.

Gwamnonin na G-5 da suka hada da Nyesom Wike, Gwamna Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da Okezie Ikpeazu (Abia) dai suna takun-saka ne da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Biyo bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar wanda Wike ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar.

Gwamnonin sun bayyana cewa an tafka kura-kurai a lokacin zaben fidda gwanin kuma sun ce dole ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu, wanda dan Arewa ya yi murabus.

Tun bayan rikicin dai ake ta rade-radin cewa kungiyar gwamnonin basa goyan bayan dan takarar shugaban kasar.

Sai dai tsohon Ministan Ilimin ya yi watsi da rahotannin inda ya bayyana su a matsayin na kanzon kurege.

Leave a Reply

%d bloggers like this: