Ministan ayyuka da gidaje Injiniya David Umahi ya bayyana cewa hanyar Abuja zuwa Kaduna ta kammala kashi 20 cikin dari kacal.
Ya bukaci kamfanin gine-ginen da su gaggauta kammala aikin nan da shekarar 2024.
A cewarsa, sashin Kaduna zuwa Zariya ya kammala, yayin da bangaren Kaduna zuwa Kano ya kammala da kashi 70 cikin 100.
Da yake magana a wata ziyarar da ya kai gidan gwamnatin jihar Kaduna tare da wasu jami’ai a wani bangare na rangadin duba aiki kan titunan gwamnatin tarayya da ake ginawa.
Ministan ya bayyana kudurinsa na bin umarnin shugaban kasa na kammala aikin akan lokaci.
Ya jaddada mahimmancin aiki mai inganci da kuma kammala aikin akan lokaci. Ministan ya tabbatar da cewa ba batun bayar da tallafin aikin ba ne jinkirin kammala aikin, yana mai cewa rashin tsaro ma ya taka rawar gani wajen jinkiri ga aikin titunan.