Hankalinmu ba zai kwanta ba har sai matsalar tsaro ta kare a Najeriya – Buratai

0 195

Shugaban rundunar sojin ƙasar nan janar Tukur Yusuf Buratai ya ce dakarun sojin kasar nan za su ci gaba da tsayuwa wurin yakar rashin tsaro a kasar nan har sai sun ga bayan hakan.

Buratai ya samu wakilcin laftanal janar Lamidi Adeosun a yayin bikin yaye sojoji karo na 79 a Zaria a ranar Asabar.

Shugaban rundunar sojin ya jajanta cewa Najeriya na fuskantar matsalar Boko Haram, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka da ke matsantawa rayuwa.

Buratai ya taya sojojin murna tare da basu shawarar aiki tukuru, kwarin guiwa, ladabi da nagarta.

“Ina so in sanar da cewa za mu ci gaba da yakar rashin tsaron da ya addabi kasar nan,” yace.

“Ana sanya ran za ku saka duk wani kwarin guiwarku wajen tabbatar da kun yi aiki cike da kwarewa.

“Ina kira gareku da ku mayar da horarwa da kuka samu ta zamo jikinku a duk inda kuka samu kanku.”

Ya ce rundunar sojin ta ba baiwa dakarun abinda ya kamata sannan tana sa ran za su yi iyakar kokarinsu a yayin gudanar da ayyukan su.

“Akwai bukatar ku sani cewa, a yau an kara karfin rundunar sojin Najeriya saboda sun samu karuwar dakaru 4,918,” yace.

“Ina tabbatar muku da cewa kun samu goyon baya daga wurinmu da kuma walwala mai dorewa.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: