Hana shigar yara mata otal zai taimaka wajen magance matsalar safarar mata a Najeriya

0 158

Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, wacce ta bayyana hakan a ranar Asabar a wajen bikin ‘Bude horo da bayar da tallafi’ da aka gudanar a Abuja, ta ce hana shigar yara mata otal zai taimaka wajen magance matsalar fataucin.

Tana mayar da martani ne kan ceto wasu ‘yan matan Najeriya goma da aka yi zargin an yi safarar su zuwa Ghana domin zaman kansu.

Kennedy-Ohaneye ta ce za a fara daukar matakin yaki da irin wadannan ayyuka, kamar fataucin mutane daga ma’aikatar harkokin mata a ranar Litinin.

Ta ce za a ba wa masu otal otal umarnin sanya alamar ‘No Lodging of Underage Girls’ a wajen wuraren su.

Ministan ta kuma bada umurci ga masu makarantu a kasar nan da su dauki mataki kan cin zarafin daga malamai ko dalibai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: