Hakimai 11 Sun Bijirewa Umarnin Gwamna Ganduje

0 255

Hakimai goma sha ɗaya ne su ka bijirewa umarnin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda ya umarci kowanne hakimi da ya zauna a masarautarsa domin yin hawan daushe.

Tun da farko gwamna Ganduje ya bayar da umarnin ne a matsayin martani ga umarnin da Sarkin Kano ya yi ga dukkanin hakimai na ƙananan hukumomi guda 44 da su hallara a birnin Kano domin yin hawan na daushe.

Umarnin Gwamnan na ƙunshi ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Abba Anwar ya sanyawa hannu, in da sanarwar ta buƙaci dukkanin hakimai da su tsaya a masarautunsu domin gudanar da bukukuwan hawan na daushe.

Sanarwar ta ƙara da cewa hakiman da su ke masarautar Kano ne kawai za su halarci hawan, amma sauran hakiman da su ke ƙarƙashin masarautun Bichi da Rano da Ƙaraye da kuma Gaya za su yi a masarautunsu.

Hakiman da su ka bijirewa umarnin gwamnan tare da shigowa masarautar Kano domin yin hawan daushen sun haɗar da; Madakin Kano Yusuf Nabahani hakimin Dawakin Tofa da Ɗan Amar Aliyu Harizimi Umar hakimin Doguwa da Dokaji Muhammadu Aliyu hakimin Garko, sai Makama Sarki Ibrahim hakimin Wudil.

Sauran su ne Sarkin Fulanin Ja’idinawa Buhari Muhammad hakimin Garun Malam, da Barde Idris Bayero hakimin Bichi da Sarkin Bai Mukhtar Adnan hakimin Danbatta, da Yarima Lamido Abubakar hakimin Takai, da kuma Dan Isa Kabiru Hashim hakimin Warawa, ragowar su ne Dan Madami Ibrahim Hamza Bayero hakimin Kiru, da Sarkin Dawaki Mai Tuta Bello Abubakar hakimin Gabasawa.

Wannan dai yana nuna yadda ake ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Masarautar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: