Jami’in hukumar jindadin alhazai ta jihar jigawa mai kula da shiyar Hadejia Alhaji Yakubu Muhammad ya shawarci maniyyata aikin hajjin bana da su lura da kayayyakinsu domin tsira daga sharrin masu sanya kwaya a kayan alhazai
Malam Muhammad ya bada wannan shawarar ne yayin rufe bitar maniyyata aikin hajjin bana da hukumar tayi a garin Hadejia.
Haka zalika jami’in ya hori maniyyatan su kauracewa karbar ajiyar mutanen da basu sani ba
Tun farko a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Hadejia Alhaji Abdullah Maikanti wanda ya samu wakilcin councilor mai wakiltar mazabar Matsaro Alhaji Adamu Yusuf, ya bukaci maniyyatan da suyi taka tsantsan da dokokin kasa mai tsarki da duk wani aiki da ka iya bata sunan kasar nan a idon duniya
Kujeru 54 ne hukumar alhazai ta jihar Jigawa ta warewa maniyyatan karamar hukumar Hadejia yana mai cewa nan gaba kadan zaa sanar dasu lokutan tafiyarsu