Hadejia: Badaru Ya Maida Martani Kan Rahoton Ambaliyar Ruwa

0 613

Gwamnatin jihar Jigawa a Najeriya tace tana dakon shawarwarin kwararru akan rahotan da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, inda ta bukaci mahukunta su sauyawa garin Hadejia matsugunni saboda barazanar ambaliyar ruwa da garin fuskanta a kowace shekara.

Rahotan binciken wadda kwamitin kwarru akan sauyin yanayi da sha’anin muhalli, karkashin kulawar majalisar dinkin duniya suka fitar yayi hasashen cewa, ambaliyar ruwa zata mamaye garin Hadejia baki dayan sa nan da shekaru biyu masu zuwa. Don haka, akwai bukatar mahukunta su dauki matakin sauyawa Hadejia matsugunni domin kare rayuwa da dukiyar al’umma.

Hasashen kwararrun wadda aka yi amfani da hanyoyin kimiyyar fasahar zamani, ya nuna su-ma garuruwan Auyo da Birniwa dake makwaftaka da garin na Hadejia na cikin yanayin barazanar mamaya daga ambaliyar ruwa.

Rahotan ya lura da tsananin ambaliyar data wakana a Hadeija a bara da-ma sauran garuruwa dake kan hanyar kogin Hadejia-Jama’are da kuma Komadugu zuwa tafkin Chadi.

Sai dai a karon farko gwamna Badaru Abubakar ya magantu dangane da wannan rahoto.

A wata gajeriyar kasida daya wallafa game da rahotan majalisar dinkin duniya akan makomar Hadejia, Arch. Aminu Kani yace, daukar matakan kare Hadejia daga barazanar ambaliyar ita ce mafita, amma ba sauyawa garin matsugunni ba, la’akari da dinbin kayan al’adu da kadarorin gwamnati dana daidaikun mutane na biliyoyin naira a garin Hadejia.

Sai dai gwamna Badaru na cewa, koda yake batun ne na amfani da ilimin kimiyya, amma lissafin kalkuleta ne zai fayyace matakin da gwamnati zata dauka bayan karbar rahotan kwararru akan wannan lamari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: