Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ba da tallafin kayan jin ƙai ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya

0 103

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ba da tallafin kayan jin ƙai mai nauyin ton 50 ga Nijeriya don taimaka wa waɗanda suka yi asarar gidaje sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru kwanan nan.

An mika kayan agajin ga jami’an gwamnatin tarayya ga hukumar kula da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ma’aikatar harkokin waje, da Ofishin mai ba da shawara kan tsaron ƙasa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Jakadan UAE a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya miƙa wannan tallafi a madadin Shugaba Sheikh Mohamed Al Nahyan, inda ya jaddada aniyar UAE na tallafa wa ƙasashen da ke fuskantar iftila’i.

A martaninsa, Dr. Ahmed Dunoma, Sakatare Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Waje, ya gode wa UAE a madadin Shugaban kasa Bola Tinubu, yana mai karfafa alaƙa tsakanin kasashen biyu.

Babbar Daraktar NEMA, Zubaida Umar, ta kuma nuna godiya ga UAE, tana mai cewa tallafin zai taimaka wajen ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa al’ummomin da ambaliyar ta shafa wajen rage raɗaɗi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: