Gwanatin jihar Osun ta rufe babbar Kasuwar Abekuta saboda yaduwar cutar amai da gudawa
Gwanatin jihar Osun ta rufe babbar Kasuwar Abekuta, domin kare al’umma garin daga yaduwar cutar amai da gudawa.
Kasuwar da ake kira da Iberekodo wacca keci a kullum, an rufe ta da nufin kare mutane daga kamuwa daga cuttuuka masu saurin yaduwa.
Wannan sanarwar na kunshe ne cikin jawabin mai bawa Gwamnan sha’awara fannin muhalli, Mr Ola Oresanya.
Inda yace gwamnatin jihar ta dauki wannnan matakin ne a wannan Kasuwar saboda yanayin rashin tsaftar ta, da kuma yanda muhallin Kasuwar ya kasance mai munin gaske wanda barazana ne ga lafiyar al’umma.
Ya kara da cewa rashin tsaftar Kasuwar zai shafi abincin da mutane suke amfanin da shi da kuma sauran kayayyakin aikin yau da kullum.
Kafin dai gwamantin jihar ta umarcin yan Kasuwar akan su kansace masu tsaftar ciki da wajen Kasuwar, amma suka ki bin umarnin.