Gwamnonin Jihohi 16 sun mika rahoton nuna goyon bayansu na samarda ‘yan sandan jihohi ga majalisar tattalin arzikin kasa.
Sun kuma ba da shawarar yin sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar nan don ba da damar kafa ‘yan sandan jihohi.
Rahotannin na daga cikin shawarwarin da aka bayar samu a taron majalisar zartarwa karo na 140 wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta a fadar gwamnati dake Abuja ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, majalisar zartaswa ta kasa tana jiran rahotanni daga jihohi 20. Al’ummar kasar nan dai na fama da tashe-tashen hankula na sace-sacen jama’a, da hare-haren ‘yan bindiga lamarin da ya sake farfado da kiraye-kirayen kafa tsarin ‘yan sanda da dama ciki har da ‘yan sandan jihohi.