Gwamnomin Babbar jam’iyyar adawa PDP sunyi watsi da shirin kafa wata sabuwar kawance domin kawar jam’iyyar APC mai mulki, a babban zaben shekarar 2027.
Wannan na daga cikin abubuwan da aka cimma matsaya a taron gwamnonin jam’iyyar ta PDP da aka gudanar a birnin Ibadan, Jihar Oyo, daga ranakun jiya Lahadi zuwa yau Litinin.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, kuma gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, shi ne ya karanta sanarwar bayan taron ga manema labarai.
Gwamna Bala ya bayyana cewa PDP na maraba da kowane mutum ko jam’iyya da ke son shigowa cikin jam’iyyar domin hada kai.
Sai dai, ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da Labour Party a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar da Peter Obi, na ci gaba da kiraye-kirayen kafa kawance domin kifar da jam’iyyar APC a shekarar 2027.