Gwamnatin Zimbabwe ta kwashe dalibai 118 daga Kasar Ukraine zuwa kasashe makwabta

0 177

Gwamnatin Zimbabwe ta kwashe dalibai 118 daga Kasar Ukraine zuwa kasashe makwabta.

An mayar da daliban zuwa Romania, Hungary, Slovakia da Poland.

An ambato ministan yada labaran kasar na cewa za a ba su tikitin jirgin na komawa gida.

Ministan ya bukaci daliban Zimbabwe da har yanzu suke Ukraine da su nemo hanyarsu ta zuwa Poland inda za su samu taimakon gwamnati.

A halin da ake ciki dai, ya zuwa yanzu wasu daliban Kenya 79 ne suka bar Ukraine bayan mamayar da Rasha ta yi.

Gwamnati ta ce dalibi daya ya riga ya isa kasar Kenya, wasu 74 kuma suna kasar Poland, biyu a Romania, biyu kuma a kasar Hungary.

Daliban Kenya hudu ba su nuna sha’awar barin Ukraine ba, saboda dalilai na kashin kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: