Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin hana zirga-zirga a kan iyakokin jihar Katsina da Sakkwato

0 262

Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da umarnin hana zirga-zirga a kan iyakokin jihar Katsina da Sakkwato daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Alhaji Mannir Haidara shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Gusau.

Ya ce wannan na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na ragewa tare da magance ayyukan sace-sacen da ‘yan bindiga ke yi, musamman a manyan titunan jihar. Don haka kwamishinan ya shawarci masu ababen hawa da matafiya da su bi wannan umarni, domin a cewarsa sun yanke shawarar ne domin kare lafiyarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: