Gwamnatin tarayya zata zamantar da gidan tarihi na Dutse

0 225

Gwamnatin tarayya ta kammala shirye shiryenta domin karbar gidan tarihi da adana bayanai dake fadar mai martaba sarkin Dutse, tare mayar da shi na zamani.

Wannan sanarwar na kunshe ne cikin bayanan ministan yada labarai da al’adu na kasa Lai Muhammad, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci birnin na dutse tare da ziyartar wannan tutar dake gonar Malam Alu dake karamar hukumar birnin kudu, domin ganin tutar da tafi kowacce tsayi a fadin kasar nan.

A cewar ministan idan an kammala gyaran gidan tarihin dake dutse, hakan zai jawo hankalin masu bude ido dake ciki da wajen kasar nan

Kafin hakan dai Mai Martaba Sarkin Dutse Dakta Nuhu Muhammad Sanusi shine ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gyara gidan tarihi na masarautar Dutse domin ya koma na zamani.


Sarkin ya bukaci hakan ne lokacin da ministan ya kai masa ziyarar ban girma a fadar sa.


Dakta Nuhu Muhammad Sanusi ya ce idan aka gyara wannan gidan tarihi na masarautar Dutse zai sake fitowa da jihar Jigawa a idon duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: