Gwamnatin tarayya zata samar da cibiyoyin koyar da sana-oi ga matasa kimanin guda uku a jihar Jigawa

0 195

Gwamnatin tarayya zata samar da cibiyoyin koyar da sana-oi ga matasa kimanin guda uku a jihar Jigawa dake arewa maso yamma.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan bunkasa tattalin arziki ta hanyar Inganta sanaoin hannu a kafar sadarwa ta zamani ,Mr Fegbo Ununubo ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Dutse Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sanusi

Yace za a samar da cibiyoyin a garin Dutse da kuma ragowar biyu a shiyoyin dan majalissar dattawa ta Jigawa ta arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas

Egbo ya kara da cewar za a horas da matasa dari biyar a  kowacce cibiya da nufin koyar dasu hanyoyin sarrafa kayayyakin gargajiya da suka hadar da takalmi da dinki da kuma Saka.

Ya ce hakan na daga cikin tsarin shugaban kasa na kyautata rayuwar yan Nigeria da kuma farfado da kayayyakin gargajiya da ake dashi a jihar jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: