Gwamnatin tarayya zata kafa hukumar ƙayyade farashin kayan masarufi a Najeriya

0 329

Gwamnatin tarayya ta ce tana aiki domin kafa hukumar ƙayyade farashin kayayyakin abinci a matsayin maslaha ga hauhawar farashin kayan masarufi a ƙasar.

Ana sa ran hukumar za ta yi nazari tare da daidaita farashin kayan masarufi da kuma kula da muhimman rumbunan abinci don daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana haka jiya Talata a wani taron yini biyu da aka yi kan sauyin yanayi da tsarin abinci da kuma tattara albarkatun kasa da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sanata Shettima ya ce taron na nuna ƙoƙarin Najeriya na rage mummunan tasirin sauyin yanayi da tabbatar da samar da abinci. Mataimakin shugaban ƙasar wanda ya yi bayani kan gyare-gyaren manufofi da gwamnati ta yi domin samar da abinci da ruwan sha, ya ƙara cewa maslaha ga matsalar abinci ya zama abu na gaggawa da matsakaici da dogon zango inda ya bayyana cewa tsarin matsakaicin zango ya ƙunshi farfaɗo da samar da abinci ta hanyar tallafi kamar rarraba taki da hatsi ga manoma da gidaje domin rage raɗadin cire tallafin mai da kuma magance banbancin farashin abinci ta hanyar kafa hukumar da za ta kula da farashin kayayyaki ta ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: