Gwamnatin tarayya zata bada taimako ta hanyoyi daban-daban ga mabukata

0 275

Ministan bada agaji da yaki da talauci Dr Betta Edu, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya zata samar da asusun tallafi da bada agaji na fadar shugaban kasa.

Betta Edu ta bayyana haka ne jiya a Abuja yayinda ta karbi bakuncin mambobin gidauniyar Bill da Melinda Bills Gate.

Ministar ta kuma yabawa gidauniyar ta Bills Gate bisa tallafin agaji da take baiwa Nahiyar Afrika,ta kma bukaci gidauniyar ta cigaba da ayyukan ta na jin kai.

Betta Edu ta tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na bada taimako ta hanyoyi daban-daban ga mabukata wanda rikici ya dai-daita a fadin kasar.

Daraktan gidauniyar a Najeriya Jeremie Zoungrana, ya tabbatarwa Ministar shirin gidauniyar Melinda na yin aiki kafada-da-kafada da ma’aikatar jin kai ta Najeriya domin taimaka mata wajen magance matsalolin jin kai a Najeriya.

Jeremie Zoungrana, ya kuma bayyana sha’awar kungiyar na yin aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma manufar bada agaji a kasar nan. Ya kuma yabawa Ministar wajen yin aiki da masu ruwa da tsaki domin bada agaji ga mabukata a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: