Gwamnatin tarayya za ta sanya tsarin Almajirci a cikin shirin ciyar da dalibai

0 208

Babbar mataimakiya ga shugaban kasa ta musamman kan ciyar da makarantun na kasa, Dakta Yetunde Adeniji, ta bayyana hakan a lokacin da ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Jigawa.

Ta ce sun kai ziyarar ne domin sanar da Gwamnan shirin Gwamnatin Tarayya na fadada shirin ciyar da makarantun kasar zuwa makarantun Almajiri.

Ta ce Tinubu na da sha’awar ganin an samar da isasshen abinci ga ‘yan makaranta a fadin kasar nan. Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya godewa hukumar SSA bisa wannan ziyara, sannan ya kuma godewa shugaba Tinubu kan yadda ya amince da ci gaba da gudanar da shirin, ya kuma kara da cewa shirin ciyar da daliban ya samu nasara da tasiri a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: