Gwamnatin tarayya za ta gudanar da gyare-gyare a hanyar Abuja zuwa Kaduna

0 82

Gwamnatin tarayya ta ce ta amince da kashe naira miliyan 366 domin gudanar da gyare-gyare a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Babbar hanyar, wadda ake sake ginawa kusan shekara shida da suka gabata, Julius Berger ne ke yi, amma yana fama da ramuka da sauran matsaloli da suke tayar da hankalin direbobi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wata sanarwa da ma’aikatar aikace-aikace ta sanar, za a fara ne da sashe na 1 na titin daga Zuba zuwa ƙaramar hukumar Tafa ta jihar Neja, inda aka ba masu kwangilar mako biyu.

“Za a cike ramuka da kuma sabunta wasu wuraren da suka lalace, inda za a kashe naira miliyan 366.”

Wannan sanarwa dai ta fito ne ƴan sa’o’i bayan da sashen Hausa BBC ya yi wani rahoto kan yadda aikin ya ƙi ci yaƙi cinweya a safiyar ranar Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: