Gwamnatin Tarayya tace za a kara tabbatar da adalci wajen rabon arzikin kasar nan
Gwamnatin Tarayya tace sabon tsarin rabon kudaden shigar kasarnan wanda zai kara tabbatar da adalchi wajen rabon arzikin kasa, zai kammalu a watan Disamba mai zuwa.
Shugaban kwamitin raba kudaden shiga na kasa, Engr. Elias Mbam wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja a karshen mako, ya ce tun shekarar 1992 rabon da a sake bibiyar tsarin rabon.
A cewarsa sabon tsarin rabon ya fi mayar da hankali ne kan rabon kudaden shiga tsakanin gwamnatin Tarayya da ta Jihohi da Kananan Hukumomi.
Engr. Mbam ya ce daga shekarar 1992, aka samu canji ta hanyar kirkiro karin wasu jihohi shida a 1996, wanda ya kawo adadin jihohi zuwa 36 sannan Kananan Hukumomi sun karu daga 589 zuwa 774, da sauran sauye-sauye.
Engr. Mbam kara da cewa tsarin rabon na yanzu shine Gwamnatin Tarayya tana da kashi 52.68 na jimlar kudaden shiga, Jihohi suna samun kashi 26.72 yayin da Kananan Hukumomi ke samun kashi 20.60 cikin 100.