Gwamnatin tarayya tace tana shirin sake fasalin kamfanin rarraba wutar lantarki na kasar nan domin yayi dai-dai da dokar kamfanin na shekarar 2023.
Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu shine ya fadi haka jiya a Abuja a wajen wani taron tsare-tsaren wutar lantarki na kasa.
Ministan yace Najeriya ta kara yawan kudaden samun ta na cikin gida zuwa Dala Tiriliyan guda nan shekarar 2030 kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsara domin kara yawan masu saka hannun jari a bangaran wutar lantarki.
Mista Adebayo Adelabu yace gwamnatin tarayya na aiki da hukumomin Jiha dana kananan hukumomi domin samar da wutar lantarki a fadin kasar nan. A cewar sa, daga cikin tsare-tsaren da za’a samar, za’a tabbatar an samar da shirin zuba hannun jari mai dorewa domin cigaban fannin.