Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kammala kasuwar zinare da ta fara ginawa a Kano nan da watanni 10

0 200

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kammala kasuwar zinare da ta fara ginawa a Kano nan da watanni 10.

Ministan tama da karafa, Olamilekan Adegbite, ya sanar da haka yayin rangadi a kasuwar da ake ginawa a Kano, kamar yadda yazo cikin sanarwar da kakakin ma’aikatarsa ya fitar.

A wani labarin kuma, kotun daukaka kara a Kano ta dage sauraron karar da ake yiwa Yahaya Sharif Aminu dan shekara 22 wanda a bara aka janye hukuncin kisan da aka yanke masa bisa zarginsa da yin batanci ga fiyayyen halitta.

Dage sauraron karar ya biyo bayan bukatar gwamnatin jihar Kano a jiya ta neman karin lokaci domin fitar da martani dangane da daukaka karar da Yahaya Aminu yayi.

Tuni gwamnatin jihar ta yi jinkirin watanni 11 kafin fitar da martaninta, kasancewar an mika mita kama bayanin wanda ake kara a watan Maris na bara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: